Dara ta fara cin gida: Majalisar dokokin Kebbi ta bukaci Dan Bagudu ya yi mata bayani dalla dalla yadda ya kashe wasu N18bn


Wasu bayanan sirri da shafin labarai na isyaku.com ya samo na nuni da cewa an sami wata yar baraka tsakanin yan Majalisar dokoki da kuma Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar Bagudu. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Bayanan na zargin cewa yan Majalisar dokokin sun aike wa Gwamna Bagudu wasika ce suna neman bayanin yadda Gwamnatin jihar Kebbi ta kashe wasu  makuddan kudi har fiye da Naira biliyon  N18bn.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da ke da sa hannun Suleiman Shamaki, mukaddashin Magatakardar Majalisar dokokin jihar Kebbi, wacce ta ce Gwamnati ta bukaci ta karbo wasu kudi daga Gwamnatin Tarayya.

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta amince Gwamnatin jihar Kebbi ta karbo kudaden daga Gwamnatin tarayya tun ranar 18 ga watan Oktoba 2021 sakamakon wasika da Gwamnatin jihar Kebbi ta aika wa Majalisar dokokin jihar mai lamba GHBK/8/21/Vol.1.


Majalisar dokokin jihar Kebbi ta bukaci Gwamna Bagudu ya bayyana a gabanta ranar Juma'a 27 ga watan Janairu 2023 domin ya yi mata bayanin yadda ya sarrafa kudaden don amfanin al'ummar jihar Kebbi.

Daga bisani ranar Alhamis 26 ga watan Janairu, Shehu Muhammad Yauri ya fitar da wani takaitaccen sanarwa da ya ke yawatawa a shafukan sada zumunta cewa "Daga mataimakin Majalisar dokokin zuwa kasa sun ajiye mukaminsu gaba daya". Ya ce.

Ana zargin wata takarda da aka wallafa tare da sanarwar, na dauke da sunayen mutane 20 har da na mataimakin shugaban Majalisar dokokin.

Bayanan sirri da muka samu na zargin cewa ana kokarin sasanta lamarin tsakanin bangarorin guda biyu wanda rinjayensu yan jam'iyar APC ne mai mulki. Lamari da ke faruwa wata daya kacal karfin zaben shugaban kasa.

Shafin labarai na isyaku.com ya tuntubi mataimakin Kakakin Majalisar dokokin jihar Kebbi kan lamarin, sai dai bai amsa kiran waya kuma bai mayar da amsar sakon kar ta kwana sms da aka aika masa ba.  

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN