Da dumin-dumi: Kotun koli ta Najeriya ta tabbatar wa Sanata Adamu Aliero da Dr. Yahaya kujerarsu na takarar Sanata a jihar Kebbi


Kotun koli ta Najeriya ta tabbatar da kasancewar Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin halastaccen dan takarar Sanata na Kebbi ta tsakiya da Sanata Dr. Yahaya Abubakar Abdullahi a matsayin dan takarar Sanata a Mazabar Sanata na Kebbi ta arewa a hukunci da ta yanke ranar Litinin 30 ga watan Janairu 2023.

Majiyarmu daga birnin Abuja ya shaida mana. Kazalika Sakataren jam'iyar people's Democrat party reshen PDP jihar Kebbi  Abubakar Bawa Kalgo ya tabbatar wa shafin labarai na isyaku.com yayin wata tuntuba kan gaskiyar lamarin. 

Hukuncin na Kotun koli na ranar Litinin ya kawo karshen jayayya kan lamarin da ya dade yana hana ruwa gudu a cikin jmiyar PDP reshen jihar Kebbi a cewar wata majiya.

Ku biyo mu don karin bayani....

Latsa nan ka karanta cikakken labari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN