Wasu mutane sun kai hari kan tawagar ɗan takarar gwamnan jihar Legas a inuwar PDP, Abdul-Azeez Adediran wanda aka fi sani da Jandor a yankin Coker, Aguda da ke ƙaramar hukumar Surulere.
Legit.ng ya wallafa cewa maharan waÉ—anda ake zaton yan daba ne sun bude wuta tare da lalata wasu daga cikin motocin Ayarin Jandor yayin harin na ranar Jumu'a 27 ga watan Janairu, 2023.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin wannan harin, yan daban sun tagka É“arma kuma sun jikkata akalla mutane uku suna Asibiti kwance.
Jandor tare da wasu mambobin PDP sun halarci taro da 'yan kasuwa da wasu ƙungiyoyi a yankin ƙaramar hukumar Surulere, jim kaɗam bayan haka ne aka kai masu hari.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a halin yanzu jam'iyyun PDP da APC mai mulki sun zargi junansu da É—aukar nauyin harin.
A wata sanarwa da kakakin APC na Legas, Seye Oladejo, ya fitar kuma jaridar Vanguard ta gani, ya ce:
"An ja hankalin mu kan wani harin ta'addanci da aka kaiwa mutanen da ba ruwansu, É—an takarar gwamnan PDP da ya fi shahara da Jandor ake zargi da É—aukar nauyi yayin kamfe dinsa a Surulere."
"Lamarin ya jikkata mutane da dama kuma mutum uku suka mutu, muna Allah wadai da lamarin da ke taɓa lafiyar talakawa da sunan Kamfe."
Haka nam kakakin PDP a Legas, Hakeem Amode, ya zargi jam'iyyar APC da É—aukar nauyin 'yan daba su farmaki ayarin É—an takarar.
"APC ta titp yan daba su ta da yamutsi a ƙaramar hukumar Surulere gabanin ziyarar da ɗan takarar gwamnan PDP ya kai gundumar ranakun Alhamis da Jumu'a."
"Maharan sun je fadar Baale na Ojuoluwa suka ja masa kunne kar ya sake ya bari a zo wajensa, suka kulle wurin. Haka nan yan daban É—auke da muggan makamai da APC ta turo sun lalata runfuna da kujerun wurin taron."
"Sun lalata kayan da aka shirya a Iponri Housing Estate kuma da yawan mambobin mu dake tsara wurin sun samu raunuka," inji kakakin PDP.
Da yake tabbatar da lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce babu wanda ya mutu a lamarin amma akwai wadanda suka jikkata.
Daga isyaku.com