An kama wanda ya yi wa yarinya yar shekara 9 mai siyar da kunu fyade a kasuwa
Illustrative picture only
Dan sanda mai bincike safeto Rachael Jacob-Osoola ranar Talata ya gawa wa Kotu a Ikeja cewa wani mutum mai suna Abdulraman Azirika, ya yi wa wata yarinya yar shekara 9 mai tallar kunu fyade.
Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito. Yarinyar tana taimaka wa antinta siyar da kunu ne kafin aukuwar lamarin a kasuwar Mile 2 da ke birnin Ikko, watau Lagos.
Yarinyar wacce aka sakaya sunanta saboda dalilan tsaro ta gaya wa Kotu cewa yayin da Abdulrahaman ya kira ta domin ya siya kunu, sai ya tura ta cikin dakinsa ya kulle kuma ya aikata lalata da ita.
Ana ci gaba da sharia'ar a gaban Kotu.
Daga ISYAKU.COM