Kwamitin yaki da ‘yan daba na Zamfara ya kama mutane 32 da ake zargi, ya kwato makamai

Kwamitin yaki da ‘yan daba na Zamfara ya kama mutane 32 da ake zargi, ya kwato makamai


Kwamitin Tsare-tsare na Yaki da ‘Yan Ta’adda a Jihar Zamfara ya ce ya kama wasu mutane 32 da ake zargi da karya dokar gwamnatin jihar.

Shugaban Kwamitin, Mista Bello Bakyasuwa ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai a Gusau ranar Talata.

Bakyasuwa ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin wani gangamin da jam’iyyar PDP ta shirya domin karbar dan takararta na gwamna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne jam’iyyar PDP ta gudanar da wani gangami domin tarbar dan takararta na gwamna, Dakta Dauda Lawal-Dare bayan wani hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wanda ta mayar da shi kan mukaminsa na jam’iyyar.

Bakyasuwa ya ci gaba da cewa, an kama wadanda ake zargin ne da laifin mallakar makamai, barna da barnatar da dukiyoyin jama’a da kuma kawo cikas ga zaman lafiya a yayin taron. 

“An kama daya daga cikin wadanda ake zargin da kona wata motar gwamnatin Zamfara.

“An kama wasu daga cikin wadanda ake zargin rike da bindigu kirar AK-47 da kuma na gida.

"Mun kwato motoci makare da 'yan bangan siyasa rike da makamai, da suka hada da bindigogi da yankan katako, da sauransu," in ji shi.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN