Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan jami’an NDLEA a Legas, duba yadda ta faru

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan jami’an NDLEA a Legas, duba yadda ta faru


Wasu ‘yan bindiga sun kai wa jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA hari inda suka bude musu wuta a hanyar Awolowo da ke Ikeja, Legas a daren ranar Litinin, 9 ga watan Janairu. Legit.ng ya wallafa.

An ce mutanen hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi suna kokarin kama wani direban wata babbar mota makare da jakunkuna na tabar wiwi, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar majiyar, maharan ana zargin jami’an tsaro ne da har yanzu ba a tantance su ba, an ce sun fasa daya daga cikin motocin da ke aiki na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi.

Majiyar ta bayyana cewa shiga tsakani da wasu sojoji suka yi ne ya hana harin haifar da zubar da jini yayin da maharan suka gudu tare da direban yayin da suka yi watsi da motar.

Daga shafin ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN