Wata babban kotun tarayyar mai zamanta a Abuja, ta dakatar da hukunchin da aka yiwa shugaban yan sanda Nigeria na daurin wata uku a gidan 'dan kande.
Legit.ng ta wallafa cdwa Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a cikin hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, ya ce akwai shaidu a gaban kotun ta da ke nuna cewa shugaban yan sandan ya bi umarnin kotun.
Umarnin kotun farkon dai shine a maido da Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritayar dole daga aikin ‘yan sanda.