Gwamnatin Najeriya tayi sabon yunkurin da ake sa ran zai kawo karshen wahalar fetur


A makon nan ne kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya dauki wasu matakan da ake ganin za su sa a samu man fetur a wadace a gidajen mai. Legit.ng ta wallafa.

Vanguard a rahoton da ta fitar ranar Laraba, 14 ga watan Disamba 2022, ta ce a jiya kamfanin NNPCL ya rage farashin sayen fetur a tasha zuwa N148.

A dalilin rangwamen da kamfanin kasar ya yi, ana sa ran farashin litar man fetur ya sauka.

Baya ga rage farashin lita a manyan tashoshin mai, NNPCL ya yi alkawarin bada isasshen man da ake bukata ga‘yan kasuwa domin fetur ya samu sosai.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan kasuwan sun koka da cewa kan N200 suke sayen duk litar man fetur daga tasoshin manyan ‘yan sarin da suke zaman kansu.

Wannan tsadar ce ta jawo ‘yan kasuwa suka gagara cika umarnin da DSS ta bada kwanakin baya, ta bada umarni kowa ya rika saida litarsa a kan N170.

A zaman da aka yi a farkon makon nan, jaridar ta ce an yi nasarar shawo kan duk sabanin da ake da su tsakanin NNPLC da masu ruwa da tsaki a harkar.

Wani babban jami’in gudanarwa na kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi ya tabbatar da wannan matsaya da aka cin ma, ya ce an yi masu rangwamen farashi.

Osatuyi yake cewa ‘yan kungiyarsu za su iya daukar fetur daga tasha a kan N148 a kowace lita, hakan zai sa su rage farashin da za su saida mai a kasuwa.

“An kyale ‘yan kungiyarmu (IPMAN) su dauki litar man fetur a kan N148, hakan yana nufin za mu iya rage farashinmu a gidajen mai.

A shirye muke mu hada-kai da sauran bangarori wajen shawo kan matsalar karancin mai a fadin kasar nan, ba tare da bata lokaci ba.”

- Mike Osatuyi


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN