Bukatu 6 da muka mika wa Buhari —Sheikh Daurawa


Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana shawarwari da nasihohin da suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari kan mastalar tsaro a ganawarsu da shi a Fadar Shugaban Kasa. Rahotun Jaridar Aminiya.

Malamin ya ce sun yi wa Buhari nasihohi kan nauyin al’umma da ke kansa sannan suka ba shi shawarwari kan matsalolin da ke faruwa a Najeriya a yayin ziyarar, wadda Minista a Ma’aikatar Ayyuka, Umar Ibrahim El-Yakub, ya jagoranci manyan malamai zuwa Fadar Shugaban Kasa.

“Mun kara tunatar da shi batun inganta tsaro da maganar tattalin arziki da kuma yin zabe lafiya, duk wanda ya ci a ba shi hakkinsa,” in ji Sheikh Daurawa.

A hirarsa da gidan Rediyon Freedom da ke Kano, malamin ya ce, “Daga cikin maganganun da muka tattauna a kai akwai batun karasa manyan ayyukan da (Buharin) ya fara wadanda za a iya karasa su kafin ya sauka.

“Sai maganar layin jirgin kasa daga nan (Kano) zuwa Abuja da kuma na zuwa Maradi (a Jamhuriyar Nijar).

“Sai kuma titi da ake yi daga nan (Kano) zuwa  Kaduna zuwa Abuja, idan zai yiwu a karasa shi kafin ya sauka.

“Sai kuma batun mai (fetur) da aka samu a Bauchi da matsalolin da suka fara biyo baya na rikici tsakanin Bauchi da Gombe, kar a zo a samu rikici irin wanda wadancan yankunan suka samu don sun samu arzikin mai.

“Mun kuma bukaci shugaban ya yi kokari a daidata tsakanin jihohin sannan a fara aikin, a kuma sa a yi masa matata a wurin, don a fara cin moriyarsa ko da bai samu karasawa ba, ya zama cewa dai an dora damba.

“Sannan an yi maganar manyan bankuna da aka zuba musu kudi musamman irinsu ‘Bank of Industry’ da kuma ‘Development Bank of Nigeria’ cewa ba sa ba wa ’yan Arewa basussuka saboda saka sharudan cewa dole sai mutum yana da kadara a Abuja, ko kuma a Legas, da kin shigar da bankunan da suke da tsarin bankin Musulunci, irinsu Jaiz da Taj.

“Wannan ya sa kusan Legas din suke samun kaso 50 na basussukan, Arewa kuma ba ya wuce kaso 17 , wanda hakan ya shafi tattalin arzikin yankin.

“Mun kara tunatar da shi batun inganta tsaro da magaanar Tattalin arziki da kuma yin zabe lafiya, duk wanda ya ci a ba shi hakkinsa.

“A takaice dai Shugaban ya nuna ya ji dadi, kuma ya ce tun farko da ana samun irin wannan gyaran a kai-akai, da ba a samu matsaloli da yawa ba.”

Daurawa ya ce Buahrin ya nuna cewa kasancewar malamai ba masu madafun iko ba ne, suna da ikon fada wa kowa gaskiya ido da ido.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN