Babbar Kotun jihar Kebbi da ke zamanta a Gwadangaji, ranar 19 ga watan Disamba 2022, ta wanke mutane hudu da aka gurfanar a gabanta bisa zargin hada baki da kashe wani matashi mai suna Abbas a Unguwar Badariya a garin Birnin kebbi.
Bayan wanke wadanda aka gurfanar, Kotun ta kuma wanke su daga zargin hada baki da kuma kisan Abbas bisa hujjojin Sharia da suka bayyana a gaban Kotu.
Sai dai Kotu ta kama wasu mutane biyu da suka shiga gidan suka saci babur roba-roba da ya jawo takaddamar. Sakamakon haka Kotu ta daure su shekara 5 tare da tarar N100.000 kowannensu, Kuma idan suka kasa biyan kudin tarar, zasu yi zaman kaso na wasu shekaru 5.
Karin bayani na nan tafe....