Abin gado ne? Kotu ta tsare wani mahauci bisa zargin yunkurin kashe mahaifinsa


Wata Kotun Majistare da ke Zariya a ranar Litinin ta ba da umarnin a tsare Musa Lawal, mai shekaru 21 mahauci a gidan yari bisa zargin yunkurin kashe mahaifinsa.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Lawal wanda ke zaune a Unguwar Karfe, Zariya da yunkurin kisan kai.

Alkalin kotun  Ramatu Dalhatu, wadda ba ta amsa rokon Lawal ba, ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari na Zariya har zuwa lokacin da ma'aikatar shari'a ta jihar Kaduna ta ba ta shawarwarin shari'a.

Dalhatu ya ce kotun majistare ba ta da hurumin yin shari’a a karkashin sashe na 240,293 da 199 na dokar shari’a ta 2017.

Ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 17 ga watan Janairu domin karin bayani.

Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, ASP Sarki Abdullahi, ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Disamba da misalin karfe 14.00.

Ya ce Muntari Musa ne ya kama wanda ake zargin sannan aka kawo shi hedikwatar ‘yan sanda ta birnin Zariya.

Ya ce an gano wata wuka mai kaifi da jini daga hannun wanda ake zargin.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da wukar wajen daba wa mahaifinsa, Lawal Danja wuka sau biyu a gefen hagu na bayansa yayin da (Danja) ke addu’a a wani masallaci a Rimin Tsiwa, Zariya.

Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 240,293 da 199 na dokar laifuka ta jihar Kaduna na shekarar 2017.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN