Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Fafaroma Benedict rasuwa yana da shekaru 95


Vatican City - Tsohon Fafaroma na Katolika, Benedict XVI ya rasu a gidansa da ke Mater Ecclesiae a birnin Vatican
. Legit.ng ta wallafa.

Kamar yadda Al-Jazeera ta rahoto, Fafaroman ya rasu a ranar Asabar 31 ga watan Disamba, yana da shekaru 31.

Rasuwarsa na zuwa ne bayan rahotanni da dama da suka fito a kafafen watsa labarai da ke nuna cewa yana fama da rashin lafiya.

Fafaroma Francis wanda ya tabbatar da rashin lafiyarsa ya bukaci mutane su masa addu'a ya samu sauki yayin da ya bayyana cewa rashin lafiyan ya yi 'tsanani'.

Benedict ne fafaroma tun Afrilun shekarar 2005 har zuwa lokacin da ya yi murabus a 2013, abin da ya bawa duniya mamaki.

A cewar New York Times, an fatan za a tafi da gawarsa zuwa St Peter's Basillica a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu inda mabiya darikar katolika za su tarbi gawar.

Amma, saboda ya yi murabus daga mukamin fafaroma, ba a tabbatar ko za a yi masa jana'iza irin ta fafaroma wanda ya mutu kan mulki ba.

Fafaroma Benedict XVI ya kafa tarihi a matsayin fafaroma na farko da ya fara yin murabus cikin kimanin shekaru 600.

Dangane da yadda za a yi jana'izarsa, Vatican ta ce nan bada dadewa ba za ta fitar da tsare-tsaren amma ta tabbatar za a kai gawarsa St Peter's Basilica inda 'mabiya darikar katolika za su tarbe shi'.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN