Yadda Shugaban Majalisar dokokin jiha da matarsa suka isa wurin bikin aurensu a Keke Napep (Hotuna)
Shugaban majalisar dokokin jihar Enugu kuma shugaban matasan kungiyar Ohaneze Ndi Igbo reshen jihar Enugu, Odo Nnamdi Emmanuel tare da matarsa sun isa liyafar daurin aurensu a cikin babur uku da aka fi sani da Keke Napep.
Odo, wanda aka fi sani da Nniodo da Celestina Chinasa, an daura auren ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, 2022 a jihar Enugu.