Ta yi zafi: Ganduje ya kori kwamishinan harkokin addini na Kano

Ta yi zafi: Ganduje ya kori kwamishinan harkokin addini na Kano


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kori kwamishinan harkokin addini na jihar Dr Muhammad Tahar Adam wanda aka fi sani da “Baba Impossible”.

Korar kwamishinan ta fito ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba.

An zargi Tahar Adam da gudanar da al’amuran ofishinsa a matsayin kasuwanci na kashin kansa, har ma da rage kwanakin aiki ga ma’aikatan ma’aikatar tare da kebe ranakun Laraba da Juma’a.

An kuma yi zargin cewa ya yi aiki ne ba tare da tuntubar juna ba kuma bai yi biyayya ga gwamnati ba.

Sanarwar ta ce;

“Korar da aka yi wa kwamishinan kuma dan majalisar zartarwa ta jihar ya biyo bayan halin rashin da’a da ya nuna a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati da ke rike da mukami, da kuma kalamai marasa tsaro.”

Gwamnan ya aike da sunan Dr Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano zuwa majalisar dokokin jihar a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN