Daga karshe: Gwamna Wike ya faɗi gaskiya kan dan takarar da G-5 ta kulla yarjejeniya da shi


Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa tawagar gwamnonin G5 na jam'iyyar PDP, ba su cimma wata yarjejeniya ba da wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a zaɓe mai zuwa na 2023. Rahotun legit.ng.

Sun ce Wike yayi hira da BBC inda yace mun yi jarjejeniya da wane da wane. Babu bidiyo ko sautin murya, amma wasun ku sun ɓata lokacin su suna sauraren waɗannan surutan."

"Baku san cewa idan ina son yin wani abu ba, zan yi shi? Baku sani ba? Kuna buƙatar kuyi jita-jita? Baku buƙatar yin jita-jita. Sunce akwai rigima amma babu wata rigima."

"Abinda yake faruwa yanzu somin taɓi ne kawai kafin zuwan rigimar dake tafe nan gaba."

"Saboda haka mutane na, ina son gaya muku cewa duk hukuncin da zan yanke, zan sanar da ku. Ba zan iya yanke wani hukunci ba ba tare da yin shawara.da ku ba. A cewar gwamnan."

A ruwayar Channels tv, gwamna Wike ya zargi Atiku da ganawa da wasu gwamnonin APC a ɓoye kuma ya gaza cika alkawarinsa na adalci da daidaito a PDP.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN