Yahaya Abubakar |
Bayanan sirri sun bulla yadda aka shirya yin amfani da wasu yan bangan siyasa domin cin zarafin wani dan jarida a jihar Kebbi. Shafin labari mai zaman kansa na isyaku.com ya ruwaito.
Wakilin Hijrah TV da Tambarin Hausa TV a Birnin Kebbi, Yahaya Abubakar, ya fuskanci kalubale daga wasu mutane yayin da yake gudanar da aikinsa ranar Litinin 21/11/2022 lokacin da aka iso harabar Kutu da wani dan soshiyal midiya da aka yi kararsa a gaban wata Kotun Majistare bisa zargin bata sunan wani dan soshiyal midiya a garin Birnin kebbi.
Sai dai wasu bayanan sirri da shafin labarai na isyaku.com ya bankado, sun yi nuni da cewa tuni aka shirya hana yan jarida da yan soshiyal midiya daukar hotunan yaron lokacin da aka kawo shi Kotu daga gidan Yari inda ya yi zaman wakafi na mako biyu domin fuskantar tuhumar da ake masa.
Wani sashe na rahotun na nuni da cewa wani yaron wani dan siyasa a jihar Kebbi, kuma wanda ake zargin ma'aikacin Gwamnatin jihar Kebbi ne, ya yi yunkurin tayar da hankali da zai iya haifar da fitina a harabar Kotun ta hanyar niyyar kwacewa tare da farfasa kyamara da kayan aikin dan Jaridan.
Bayan fuskantar mutanen da suka kalubalance shi, Yahaya ya kawar da ido kan lamarin, mataki da ya kai ga dakile mumunan yanayi da yaron dan siyasan ya so ya haddasa a harabar Kotu.