Eric Okunna, wani kwararren likitan mata, ya ce alfano da ke tattare da kwanciyar aure mai nagarta ba zai misaltu ba, rahotun The Cable.
A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, likitan ya tambayi ra'ayoyin wasu mazauna Awka, Jihar Anambra, kan batutuwan da suka shafi rayuwar aure musamman kwanciyar aure.
Ya ce wadanda suka amsa tambayoyinsa sun ce bai dace ma'aurata su rika hana juna hakkin kwanciyar aure ba musamman mata ga mijinta.
Okunna ya ce wasu sun ce namiji ne shugaba a gidansa don haka bai dace a rika masa wasa da 'hankali' ba.
Ya ce ingantacciyar kwanciyar aure na karfafa soyayya tsakanin ma'aurata.
Ya kuma ce yawan neman kwanciyar aure daga bangaren na miji 'ka iya jefa mata cikin wani yanayi' hakan kuma ya janyo wa namijin cutuwa.
Okunna ya ce yana da muhimmanci a rika daukar aure a matsayin abu mai muhimmanci, don haka, kada mata su rika azabtar da mazansu ta hanyar hana su kwanciya da su.
Kwararren likitan ya kara da cewa bai kamata a rika amfani da kwanciyar aure a matsayin abin ramuwar gayya ba idan an samu matsala tsakanin mata da miji.
Fa'idar kwanciyar aure a tsakanin mata da miji, in ji likita
"Kwanciyar aure kansa magani ne da ke kwantar da hankali da kallubalen rayuwa kamar damuwa, shauki kuma motsa jiki ne da ke inganta lafiya," in ji Okunna.
"Rashin jituwa tsakanin masoya ba sabon abu bane har da ma'aurata. Ba dai-dai bane ma'aurata su rika hana juna kwanciyar auren idan sun samu rashin jituwa."
"A maimakon hakan, a rika amfani da kwanciyar aure don warware matsala tsakanin mata da miji saboda yana iya kwantar da hankula a maimakon abin raba kai.
"Kauracewa kwanciya da juna a aure ba hanya bace mai kyau na warware matsaloli a aure kuma kan iya sanadin mutuwar aure."
A cewar likitan, a rika yin kwanciyar auren dai-dai gwargwado ta yadda ma'auratan za su gamsu su yi maganin kadaici.
Legit