Wani direban da ba a bayyana sunansa ba ya yi kokarin tserewa bayan da ya sha man N3000 a gidan, inda ya lalata wasu ababen hawa tare da kashe mutum daya da ke kan hanya. Legit.ng ta wallafa.
Wannan mummunan yanayi ya faru ne a jihar Kaduna da daren ranar Talata 29 ga watan Nuwamban 2022.
Sarkin Mota, wani ma'aboci Twitter da ya bayyana kansa a matsayin mataimakin dan takarar gwamnan PDP a jihar kan harkokin yada labarai ne ya yada bidiyon a kafar sada zumunta.
Ya rubuta cewa:
"Direba ya siya man 3k jiya da dare sai ya fece a guje ba tare da ya biya ba, daga baya motar da fi karfinsa ra buge wasu motocin da ke wurin har abin takaici hakan ya kai ga mutuwar wani. Allah ya jikanshi."