Kuma dai: Hatsarin mota ya sake rutsawa da ayarin motocin Gwamnan Arewa mutum 4 sun mutu


Motar Toyota Hilux da ke dauke da tawagar 'yan banga da ke rakiyar Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri yayin da ya nufi garin Mubi domin gudanar da yakin neman zabe, ya yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.

Hadarin ya afku a kusa da Fadamareke, a karamar hukumar Hong, kuma jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin na da alaka da tsananin gudu da wuce gona da iri yayin da ake kan hanyar lankwasa mai hatsari.

Bako Kaura, shugaban jami’an tsaro na jam’iyyar PDP, da wani da aka bayyana sunansa da Adamu, da kuma dan Kaura, sun mutu a hadarin.  An ajiye gawarsu a dakin ajiyar gawa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Hong.

Wasu mutane biyar da ke cikin motar da suka samu raunuka daban-daban, an kai su a cikin motar daukar marasa lafiya ta gidan gwamnati da wata motar kirar Hilux da ba ta da lamba, domin yi musu magani a wata cibiyar lafiya.

Likitan gwamna Fintiri na kashin kansa kuma shugaban asibitin gidan gwamnati, Dokta William Teri, wanda yana cikin wadanda suka fara kai dauki a hatsarin ya kuma kai wadanda abin ya shafa asibiti domin yi musu magani.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wata majiya ta shaida wa jaridar;

“Na fitar da gawarwaki guda uku da ba su da rai, amma akwai na hudun da nake ganin ya suma saboda raunin da ya samu.  Kimanin mutane tara ne a cikin motar Ramp 2 Hilux van hatsarin ya rutsa da su.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fintiri ya tsira daga mutuwa.  Wata babbar mota ta rasa yadda za ta yi ta kutsa kai cikin ayarin motocinsa dake tsaye.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN