Tsohon shugaban jami’ar Gusau zai sha ɗaurin shekara 35


Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke wa tsohon shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba hukuncin ɗauri na shekara 35. BBC ta ruwaito.

Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu, wadda ta yanke hukuncin ta ce an samu farfesa Garba ne da laifuka biyar da suka jiɓanci amfani da ƙarya wajen karɓar kuɗi da kuma zamba.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar gaban kotu a ranar 12 ga watan Oktoba tana zargin sa da tatsar kuɗi daga wani mutum bisa alƙawarin ba shi kwangilar katange jami’ar, wadda kuɗinta ya kai naira biliyan uku.

A lokacin da ta yanke hukunci, mai shari’ar ta ce ta gamsu da bayanan da EFCC ta gabatar, sannan ta yanke masa hukuncin jimillar shekaru 35 a gidan maza.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN