Hukumar NIS jihar Kebbi ta ceto wasu yara yan mata guda biyu daga masu safara


Hukkumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) reshen jihar Kebbi, ta ceto wasu ‘yan mata biyu iyayensu daya daga hannun masu safarar mutane a hanyarsu ta zuwa kasar Libya daga Sakkwato. Jaridar daily trust ta ruwaito.

Kananan yaran biyu-Faisal Rahman, 15;  da kuma Aliya Rahman mai shekaru 16 da ake jigilar su daga yankin Shagamu da ke jihar Ogun zuwa Sokoto kan hanyarsu ta zuwa kasar Libya, jami’an hukumar NIS da ke sintiri a garin Yauri a jihar Kebbi, suka tare su.

Kwanturolan hukumar NIS na jihar, Rabi Bashir Nuhu, a lokacin da take zantawa da manema labarai, ta ce ‘yan matan a lokacin da ake yi musu tambayoyi sun bayyana cewa iyayensu da ke zaune a Shagamu, suna sane da tafiyarsu zuwa kasar Libya.

"Sun ce 'yar uwarsu, wacce suka ce tana zaune a Libya, ta shirya daukarsu a Sokoto tare da izinin iyayensu a Shagamu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN