Gwamnan jihar Sokoto kuma darakta-janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku/Okowa, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa zai dauki mataki kan Gwamna Nyesom Wike da ma'aikatan sa na G-5 idan suka bayyana wanda za su marawa baya a zaben shugaban kasa. Legit.ng ya ruwaito.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa jam'iyyar a shirye take ta yi amfani da dukkan hanyoyin da za a bi wajen fadakar da duk wani mambobinta da suka yi kuskure.
Gwamna Tabuwal ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba.
Jawabin nasa na zuwa ne bayan ganawar da Gwamna Wike ke jagoranta na G-5 da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu a birnin Landan.
An jiyo Gwamna Tambuwal a cewar PM News yana cewa:
"Abokan aiki guda biyar masu kyau da ke cikin G-5…. Ka sani, koyaushe ina faÉ—in haka: muna shiga aikin injiniyan siyasa da tattaunawar siyasa. Ba yaki bane.
“A koyaushe ina gabatar da cewa a cikin wannan kasuwancinmu, duk abin da kuke yi, ko da kuna Æ™oÆ™arin É“oye shi, zai fito. Ba za ku iya tsarawa da aiwatar da aikin siyasa a cikin É—akin kwanan ku ba. Dole ne ku fito da shi
“Don haka, lokacin da abokan aikina suka yanke shawarar abin da za su yi, ina ganin a lokacin ne jam’iyyar za ta mayar da martani kan duk wani matsayi da suka dauka.”