Makiyaya da manoma sun yi fada, an kashe mutum 8 har da yara, an kone gidaje 47 a jihar Arewa


Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar ya ce akalla mutane takwas aka kashe tare da kone gidaje 47 a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya saboda shiga gonaki a karamar hukumar Bayo ta jihar. Legit.ng ta ruwaito.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 3 Disamba, 2022 a wani taron da shuganannin kungiyar Miyetti Allah da ta manoma a birnin Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, mutane takwas da aka kashe sun hada da kananan yara uku, inda yace lamarin ba karamin abin damuwa bane ga hukumomin tsaro a jihar.

Ya kuma shaida cewa, a karshen taron da aka gudanar, za a samar da hanyoyin dike barakar ta hanyar sanya ido kan makiyaya da ke kaura a yankin.

Umar ya bayyana cewa, an kama wasu da ake zargi da hannun a wannan aika-aikata, kuma an kaisu kotu domin gudanar da bincike da kuma hukunta masu laifi.

Wadanda suka halarci taron

An ruwaito cewa, wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin hukumomin tsaro, manyan jami’an gwamnati da shugabannin kungiyoyin biyu da suka samu sabani.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah MACBAN, Ahmadu Musa-Karube ya ta’allaka faruwar lamarin ga yawaita nome hanyoyoyin shanu a cikin dazuka, Punch ta ruwaito.

A cewarsa:

“Shanu ba firewa suke ba, dole su samu hanyar wucewa, amma sau tari za ku ga manoma sun nome hanyoyin shanu. Magana ta gaskiya, akwai bukatar magance hakan cikin gaggawa.”

Har ila yau, wakilin manoma, Hassan Musa, shi ma yace tabbas za a daina noma hanyoyin shanu, amma akwai bukatar gwamnatin jihar ta haramta kiwo cikin dare.

Ana yawan samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya, musannan a karshen damina lokutan da ake dauke amfanin gona.

Makamancin irin wannan rikicin ya faru a jihar Kano, inda aka samu asara da yawa a wasu kayuka sama da 10 a jihar

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN