Karyane: Gwamnoni 36 sun yi martani, sun fadi yadda Buhari ya jefa Najeriya cikin talauci


Gamayyar gwamnonin Najeriya a jihohi 36 sun bayyana kaduwa da shiga mamakin yadda aka kakaba musu laifin jefa kasar nan cikin matsanancin talauci, BBC Hausa ta ruwaito.

Karamin Ministan kasafin kudi, Clem Agba ne ya bayyana wa duniya cewa, gwamnonin Najeriya ne suka jefa kasar cikin matsanancin talauci ba wai shugaba Buhari ba.

Ministan ya fadi hakan ne a wani taron da aka gudanar, inda ya yi tsokaci game da rahoton hukumar da ta fitar da rahoton talauci a kasar nan.

Idan baku manta ba, hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar jerin jihohin da suka shiga taskun talauci a kasar nan, inda aka yi jeren daidai da yanayin da jihohin kasar ke ciki.

A cewar kididdigar, akalla mutum miliyan 139 ne a kasar ke fama da matsanancin talauci, wanda ke wakiltar kashi sama da 63% cikin 100% na jumillar 'yan kasar.

Ba laifin mu bane, laifin gwamnatin tarayya ne, inji gwamnonin Najeriya

Da suke martani ga kalaman karamin ministan ta bakin kungiyarsu, gwamnonin sun fitar da sanarwar da ke nuna fushinsu da abin da aka jingina musu, wanda a cewarsu ba haka yake ba.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai ta kungiyat gwamnonin Najeriya, Abdulrazaque Bello-Barkindo ta ce bai kamata ministan ya yi irin wadannan kalamai ba.

Hakazalika, kungiyar ta bayyana balo-balo cewa, sam babu alamun gaskiya ko miskala-zarratin a kalamansa.

Da suke fashin baki ga kamalansa, sun ce maganar wai sun watsar da al'ummar karkara a jihohin ba magana ce mai makama balle tushe ba.

Daga karshe gwamnonin sun ce, laifin gwamnatin tarayya ne a gazawarta wajen kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar, hakan ya jawo haihawar talauci, TheCable ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN