Mutumin kirki: Gwamna Buni ya ba da umarnin a saki karamin yaro da aka kama da laifin zaginsa a shafukan sada zumunta


Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayar da umarnin a saki Umar Garba dan shekara 16 da aka kama da laifin zaginsa a shafukan sada zumunta.

Mamman Mohammed, Babban Daraktan Yada labarai na Gwamna Buni ya yi ikirarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, ya ce Gwamanan bai da masaniya game da kama karamin yaron da ‘yan sanda ke tsare da shi sama da kwanaki 10.

Buni ya kuma bayyana cewa ba lallai ba ne a kama wani saboda zagi ko sukar sa.

Sanarwar ta ce;

"Wannan shine farashin shugabanci kuma muna sane da shi, saboda haka, ba zan iya ba da umarnin tsare kowa ba ko kuma la'akari da tsare kowa.

"Har sai wani ya ja hankalina game da lamarin, ban san da cewa an kama shi da tsare shi ba, yanzu na ba da umarnin a sake shi nan take."

Sanarwar ta kara da cewa yayin da gwamnatin Buni ke tafiyar da tsarin budaddiyar gwamnati, gudummawa da suka ya kamata su kasance masu inganci da ma'ana.

An kuma bukaci masu amfani da shafukan sada zumunta da su kasance masu natsuwa da kuma dau nauyin mutunta hakkin kowa da kowa, jam'iyyun siyasa, bambancin addini da zamantakewa musamman yayin da ake ci gaba da yakin neman zabe.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN