Legas: Rikici ya kaure tsakanin 'yan sanda da sojojin ruwa, an halaka ASP


Legas - Wani ‘dan sanda mai mukamin ASP a cikin ranakun karshen makon nan ya sheka barzahu bayan sun yi arangama da wani jami’in sojan ruwa a Legas tare da wasu ‘yan sanda wadanda suka caka masa wuka. Legit ta wallafa.

Wasu mutum uku dake wucewa sun samu raunika daban-daban a sassan jikinsu sakamakon artabu da suka yi a birnin Legas. 

Wannan rikicin ya haifar da hatsaniya mai rikitarwa wacce ta saka tsoro a zukatan masu shaguna wadanda suka tsere gudun abinda zai iya kaiwa ya kawo.

Mutane da yawa sun samu rauni yayin da jami’an sojan ruwan suka farmaki masu wucewa da suka so shiga tare da sasanci tsakanin jami’an tsaron.

Wani mai motar haya, Steven Ogbodeto, yace ya ga ‘yan sanda masu sintiri suna hayaniya kan lamarin da bai sani ba tare da wasu sojojin ruwa.

Yace dole ta sa ya tsaya ya ga ko zai iya sasanci a tsakaninsu amma sojan ruwan ya rikice tare da fara cakumar ‘dan sandan.

Wani jami’in ‘dan sanda wanda yayi magana da bukatar a sakaya sunansa saboda bashi da hurumin magana ga manema labarai, yace:

“Jami’in sojan ruwan ya sokawa jami’an mu wuka. Da gaggawa muka hanzarta kwashe jami’an mu tare da wasu mutum 3 masu wucewa zuwa asibitin Adeyemi amma ASP Abion bai tashi ba saboda likita ya tabbatar da cewa rai yayi halinsa. Sai dai sauran jami’an da wasu mutum 3 da aka soka an duba su tare da sallamarsu.

“An kama biyu daga cikin sojojin ruwan yayin da sauran biyu ba a kama su ba amma mun kai rahoto zuwa hukumomin soja domin a kamo sauran biyun.”

Hukumar Yan sanda ta magantu.

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ‘yan sandan na kan aikinsu yayin da sojojin suka farmake su.

Ya kara da cewa ana bincike kan lamarin.

Yace an mika lamarin hannun hukumar binciken manyan laifuka dake Panti a Yaba ta jihar Legas yayin da gawar mamacin aka ajiyeta.

Hukumar soji tayi magana

Sai dai mai magana da yawun sojin ruwa na yammaci, Edward Yeibo ya sanar da Daily Trust cewa cunkoson kan titi ne ya hada jami’an fada da wasu ‘yan sanda.

Yeibo mai matsayin kwamanda a rundunar sojin ruwa, yace a yayin haka ne ‘yan sandan tare da wasu bata garin suka fara dambatar sojojin.

“Wasu ‘yan sanda sun sake bayyana a babur kuma suka fara harbi. A halin yanzu ana bincike a kai domin tabbatar da tushen lamarin. Za a bayyana makomar binciken ga jama’a.”

- Yace.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN