2023: Fitaccen Dattijon Arewa ya fasa kwai, ya fadi yan takarar shugaban kasa 2 da ba zasu iya kashe kudin da suka tara ba


Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu; da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, basu da isasshen lokacin kashe kudaden da suka tara. Legit ta ruwaito.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a shirin Sunday Politics na Channels TV a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.

Atiku mai shekaru 76 da Bola Tinubu mai shekaru 70 sune kan gaba a takarar shugaban kasa na 2023 daga manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu.

APC da PDP kudi suka iya rabawa amma basu iya shugabanci mai kyau ba

A cewar abokin takarar Peter Obi, jam'iyyun APC da PDP suna da tsari na raba kudade amma ba wai na gudanar da shugabanci nagari wanda zai gyara rayukan al'ummar kasar ba.

Baba-Ahmed ya ce:

"Babu abu mai kama da wannan a matsayin tsari; batu ne na mutane da ke son karbar kudaden da suka tara. Dole wani ya karbi wadannan kudaden; ba zai yiwu ku barsu su tafi da wannan kudin ba.

"Tinubu bai da isasshen lokaci a rayuwarsa da zai gama kashe wadannan kudaden. Atiku bai da isasshen lokaci a rayuwarsa da zai gama kashe duk wadannan kudaden.

Don haka suna bukatar kashe shi a zaben 2023. Kuma mutane, idan kana da kudaden kashewa, za su karbe abin su."

Ya jaddada cewar LP na da kaya amma ba za ta kashe kudaden da ba za ta iya bayar da bayani a kansu ba.

Ya kara da cewar manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu suna da abun da ake kira tsari ba tare da shugabanci ba kasancewar sun yi mulkin kama karya a Najeriya tun 1999 lokacin da kasar ta samu yancin kai.

"Jam'iyya daya ce take da tsari na gaskiya, kuma ita ce Labour Party."

Tun 1999 PDP ta samar da shugabannin kaaa uku, Olusegun Obasanjo, Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan wadanda suka yi shekari 16 kafin gwamnatin APC na shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya karbi mulki a 2015.

Buhari bai damu da takarar Bola Tinubu ba, Inji Datti Baba-Ahmed

A gefe guda, mun ji a baya cewa Datti Baba-Ahmed ya ce duk da rawar ganin da Bola Tinubu ya taka wajen ganin ya yi nasara a 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da takarar tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN