Karancin man fetur: DSS ta baiwa dillalai sa'o'i 48 su daina karancin man fetur ko kuma su fuskanci fushin FG


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta umurci duk hukumomin da ke da ruwa da tsaki a aikin rabar man fetur a Najeriya da su yi kokarin kawo karshen matsalar karancin man fetur a cikin sa’o’i 48 ko kuma su fuskanci fushin gwamnati.

Hukumar ta DSS ta bayar da wannan umarni ne bayan wani taro da hukumar ta yi da duk masu ruwa da tsaki a harkar samar da mai a hedikwatar DSS da ke Abuja a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, kakakin hukumar DSS, Dr.Peter Afunanya, ya ce hukumar za ta dauki matakin tunkarar wadanda ke kokarin yin amfani da karancin man fetir wajen yin barazana ga tsaron kasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN