Innalillahi: Wasu ‘yan bindiga sun kai hari asibiti inda suka sace jarirai hudu


Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wani asibitin haihuwa da ke unguwar Nkpologwu a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra inda aka yi zargin sun yi awon gaba da jarirai hudu da aka haifa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa al’ummar yankin sun yi ikirarin cewa harin ya faru ne a daren ranar Talata, 6 ga watan Disamba. An rahoto cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki asibitin inda suka tafi da jariran ba tare da kai wa wani hari ko kashe wani ba.

Har yanzu dai ba a san dalilin sace jariran ba.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya  ce har yanzu rundunar ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.

Shima da yake mayar da martani ga rahoton, babban shugaban garin, Ferdinand Ezeiruaku ya ce irin wannan abu bai taba faruwa a cikin al'umma ba.

“Babu wani abu makamancin haka.  Bai taba faruwa ba.  Ban san yadda ya samo asali ba amma bai taba faruwa ba.  Ban san yadda bayanin ya fara ba amma ba mu taba jin wani abu makamancin haka a cikin wannan muhalli ba,” inji shi

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN