Inna lillahi: Babbar mota ta murkushe mutum 12 har Lahira bayan ta kwace a jihar Arewa
Hadarin ya afku ne a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba, 2022, yayin da wata babbar mota ta rasa yadda za ta yi, ta afkawa wasu direbobin tankar da ke jira a bakin hanya, sakamakon lalacewar hanyar Agaie-Lapai.
Shugaban karamar hukumar Agaie, Ibrahim Sayuti, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata, ya dora alhakin hadarin a kan lalacewar hanyar Agaie-Lapai.
A cewar shugaban karamar hukumar, hadurran sun zama ruwan dare a wannan hanyar.
“Wannan ba shi ne karo na farko da hakan ke faruwa a wannan shekara ba. Mun samu yanayin yadda tankar mai dauke da man fetur ta yi kasala da konewa inda aka yi hasarar rayuka da dama," in ji shi.
“Haka zalika yanayin hanyar yana shafar harkokin tattalin arzikin kananan hukumomi domin ita wannan hanya ita ce hanya mafi sauki da ta hada yammacin Najeriya da jihohin Arewa”.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta tarayya a jihar Neja Kumar Tsukwam, ya ce hatsarin ya faru ne a bisa kuskure.
Ya tabbatar da cewa mutane 12 sun rasa rayukansu.