Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na kasa, Baba Ngelzarma, ya zargi shugaba Buhari da yin watsi da makiyaya a kasar nan duk da irin goyon bayan da suka ba shi a zaben 2019 da ya gabata.
Ngelzarma wanda shi ne tsohon sakataren kungiyar kafin zaben sa a matsayin shugaban kungiyar, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Asabar, 18 ga watan Disamba. A cewarsa, gwamnatin Buhari ta ware makudan kudade ga sauran bangarorin noma. a kasar kuma ya mayar da kiwon dabbobi gefe.
“A jajibirin zaben da ya kawo Buhari karo na biyu, mun amince da shi. Mun nuna wa duniya cewa muna tare da shi, amma har ya zuwa yanzu da nake magana da ku, ba a yi kome ba.
Buhari ya yi watsi da makiyaya. Wannan a fili yake, ko Buhari ko mukarrabansa, gwamnati ta yi watsi da makiyaya. A cikin shekaru takwas da suka gabata, babu wani abu da za a iya gani… yayin da aka kashe sama da Naira biliyan 500 wajen aikin noma, ba a kashe komai kan kiwo, kusan komai ba.
Ku je ku duba duk tanade-tanaden kasafin kudin gwamnatin jihar ciki har da tanadin kasafin kudin gwamnatin tarayya. Idan ka ga abin da aka yi kasafin kudin dabbobi, za ka yi mamaki.
An yi watsi da dabbobi gaba daya”.
Ya kara da cewa duk da cewa kungiyar ta yi farin ciki da shirin sauya fasalin kiwo na kasa (NLTP), ko kadan ba zai yi komai ba wajen magance matsalolin makiyaya.
“A kwanan nan ne gwamnatin Buhari ta fara aiwatar da shirin sauya fasalin dabbobi na kasa (NLTP) inda wasu jihohi suka samu tallafin Naira biliyan uku da biliyan 6.
Wasu jihohi ne suka fara shi, wanda a Yola aka fara amma muna ganin aikin da ba zai iya magance matsalar ba.
Ta yaya kuke ganin cibiyar kiwon dabbobi da ba za ta iya daukar shanu sama da 20,000 ba za ta iya magance matsalar shanun da suka haura miliyan biyu a Adamawa? Amma a matsayin abin ƙira, ba shi da kyau, muna godiya da shi. Akalla makiyaya za su ga yadda za a zamanantar da kiwo.” Inji shi