Attajirin nan na Kano, A.A Rano ya sayi Jirgin N4.2bn don fara jigilar fasinjoji


Kano: Kamfanin jiragen sama na Rano Air a Najeriya ya samu cikakkiyar amincewar fara aiki daga gwamnatin tarayyar Nigeria. Legit.ng ta wallafa.

Kamfanin ya nemi lasisin sufurin jiragen sama (ATL) tare da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nigeria (NCAA) a cikin watan Janairu don gudanar da ayyukan jigilar fasinja da kayayyaki kamar yadda aka tsara a ciki da wajen Najeriya.

Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai da sadarwa na zamani, ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba, 2022, cewa an samu cikakken ikon fara yi.

Ya kuma bayyana cewa yanzu haka an shirya yadda kamfanin zai fara jigilar fasinjoji a fadin kasar nan.

Ya rubuta:

"Rano Air, daya daga cikin sabbin kamfanonin jiragen sama na Najeriya, wanda aka kafa a shekarar 2019, ya samu amincewar Gwamnatin Tarayya don gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na gida a garuruwan Legas, Kano, Abuja, Kaduna, Sokoto, Gombe, Yola, Maiduguri, da Asaba."

Tarihin Rano Air

Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, Shugaban Kamfanin AA Rano kuma dan asalin Kano , shine mamallakin Rano Air.

Shigowar Rano a harkar sufurin jiragen sama zai daga tare habaka tattalin arzikin Najeriya.

A shirye-shiryen gudanar da aikin Rano Air, Dailytrust ta ruwaito cewa ya samu jirage wanda suke da lamabar EMB-145LRs guda hudu don fara aiki awannan shekarar.

Binciken da Legit.ng ta yi ya nuna matsakaicin farashin Embraer ERJ-145LR da ake sayarwa a GlobalAir.com ya kai dalar Amurka $2,395,000 (N1.09 biliyan).

Haka kuma Rano ya samu nasarar karbar lasisin zirga-zirgar jiragen sama (ATL) daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).

Ana sa ran kamfanonin jiragen saman nasa zasu ringa jigilarfasinjoji da kaya daga jihohin Legas, Kano, Abuja, Kaduna, Sokoto, Gombe, Yola, Maiduguri da Asaba.

Tarihin Rano

An haifi Alhaji Auwalu Abdullahi Rano wanda aka fi sani da A. A Rano a ranar 9 ga watan Yuni 1944 wanda ya fito daga yankin Hausa-Fulani da ake kira Lausu a karamar hukumar Rano a Jihar Kano Najeriya.

Ya samu kudinsa ne daga bunburutun man fetur wanda ya fara a tun a shekara ta 1994.

wani rahoton ya nuna cewa ya gina kantunan sa na farko a jihar Kano a shekarar 1996, sannan ya kafa kamfanin A. A Rano Nigeria Limited a shekarar 2002.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN