Kotu ya umarci a tasa keyar Kwanishinan jihar APC zuwa Kurkuku


Zamfara - Babbar Kotun jihar Zamfara mai zama a Gusau, a ranar Litinin ta garƙame kwamishinan noma da albarkatun ƙasa na jihar, Alhaji Ibrahim Magayaki, bisa rashin ɗa'a ga Kotu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Alkalin Kotun mai shari'a Bello Shinkafi ya ba da umarnin a iza ƙeyar kwamishinan zuwa gidan Gyaran hali da ke garin Gusau.

Alkalin yace Kotu ta dogara da tanadin sashi na 9 na kundin dokokin Fenal Code biyo bayan matakin kwanishinan na ƙin biyayya ga umarnin Kotu.

Mai Shari'a Shinkafi yace Kwamishinan ya raina umarnin da Kotu ta bayar a shari'ar da ta gudana tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da kamfanin Dumbulum Investment.

A cewar Alƙalin, Dumbulum Investement sun samu sahalewar Kotu na haɗa wa da wasu kadarorin gwamnati cikinsu har da manyan Motoci.

Shinkafi ya bayyana ceqa duk da haka Kwanishinan Noma ya sa ƙafa y shure umarnin Kotu kana ya sayar da wasu sassan Motocin waɗanda suna daga cikin waɗanda umarnin Kotu ya shafa.

A halin yanzun, Misbahu Salauddeen, lauyan masu kara ya shaidawa manema labarai cewa matakin É—aure kwamishina da Kotu ta É—auka ya samo asali ne daga bukatar waÉ—anda yake kare wa.

Lauyan wanda aka É—aure, Mr M. S Sulaiman, yace Antoni Janar na jihar Zamfara bai sahale masa da zanta da 'yan jarida ba.

Daga nan sai Alƙalin Kotun ya ɗage zaman zuwa ranar 16 ga watan Disamba, 2022 domin a dawo a ci gab da zaman shari'ar.

A wani labarin kuma

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN