Siyasar Kebbi: Matashi Malami Jabbo ya kafa tarihi, ya jagoranci kafa kungiya ta farko don wani muhimmin bukatar dan Bagudu a 2023 (Hotuna)


"Bagudu 3rd Term for Senate" sabuwar kungiyar ce ta nuna goyon baya ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu don komawa Majalisar Dattawan Najeriya da wani matashi mai suna Malami Jabbo ya kafa a garin Birnin kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

An kaddamar da kungiyar ne ranar Lahadi 11 ga watan Disamba 2022. Lamari da ya sami magoya baya a Unguwar bye pass shiyar makarantar Dr. Amina a Birnin kebbi da kewaye Kuma ya zama mafari ga kasancewa sananniyar kungiyar farko da ta fara wannan hidima a jihar Kebbi gaba dayanta.


Malami ya ce shi kam magoyi bayan Gwamna Bagudu ne, kuma ya yi amfani da lokacinsa da kuma dukiyarsa wajen ganin ya ba Gwamna Bagudu gudunmuwarsa wajen ganin ya yi nassara a harkokinsa na siyasa .

Malami, yayin tattaunawa da shafin isyaku.com ya ce a shirye yake a ko da yaushe ya bayar da nashi gudunmuwa matukar bukatar haka ta taso.  Idan baku manta ba, Malami ne ya rubuta wani shahararren kasida da ya yi wa take "Bagudu the silent achiever" wanda Malami ya dauki nauyin buga shafin a Jaridar "The Sun" kuma aka wallafa labarin yan shekaru da suka gabata.

Yanzu dai matashin ya kuma sa an buga postocin "Bagudu for Senate 3rd Term" guda 500 zaman gudunmuwarsa da nuna kauna ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu don ganin ya shige zauren Majalisar Dattawan Najeriya bayan ya kammala wa'adinsa na mulkin jihar Kebbi a zaman Gwamna a 2023.

Latsa kasa ka kalli bidiyo

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid0CxsnLn9x387VyqcKVrqqFnanifAddkjsnoFe8a5rBrJn17V3SJDEd3e6KN51TUxel&id=100066486892301&mibextid=Nif5oz

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN