Wani abin al'ajabi ya faru a Uganda a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, yayin da wani yaro É—an shekara 2 mai suna Iga Paul ya tsira daga harin da wani dorina.
Legit.ng ta wallafa Dorinar (Hippo), a cewar rahoton CNN, ya kai wa yaron hari, inda ya hadiye rabin jikinsa kafin ya tofar da shi.
An kai harin ne a ranar 4 ga watan Disamba da misalin karfe 3 na yamma agogon kasar a gundumar Katwe-Kabatoro da ke kudu maso yammacin kasar ta Afirka ta gabas.
Paul yana wasa ne a gidansu da ke Rwenjubu cell, Lake Katwe, lokacin da lamarin ya faru.
Wani mai suna Chrispas Bagonza ya yi jajircewa ta hanyar jifan dabbar mai haÉ—ari. Jifa da Bagonza ya yi ya tsoratar da hippo kuma ya sa ta saki yaron daga bakinta, a cewar ‘yan sanda.
"An dauki bajintar wani Chrispas Bagonza, wanda ke kusa, ya ceci wanda abin ya shafa bayan ya dinga jifan hippo din ya tsoratar da shi, lamarin da ya sa ya saki yaron daga bakinsa," in ji 'yan sandan.
Iga Paul ya garzaya zuwa asibiti bayan ya tsira daga fargabar hippo
Bayan Hippon ya saki Paul, an kai yaron mai sa'a zuwa wani asibitin da ke kusa saboda raunin da ya samu a hannu daya.
Daga baya an kai shi asibitin Bwera da ke yammacin Uganda don ci gaba da kula da shi.
Paul ya kuma samu rigakafin kamuwa da cutar sankarau, kafin ‘yan sanda su mika wa iyayensa bayan an sallame shi daga asibiti.
Yan sandan Uganda sun gargadi mazauna garin
Rundunar ‘yan sandan ta ce duk da cewa hippo din ya tsorata ya koma cikin tafkin, duk mazauna kusa da wuraren da dabbobi da wuraren zama su sani cewa namun daji na da matukar hadari.
A cewar sanarwar, dabbobin daji bisa ilhami na kallon dan Adam a matsayin barazana kuma duk wata mu’amala na iya sa su aikata wani abu na ban mamaki ko kuma tada hankali.
Hippo yana daya daga cikin dabbobin da ke da hatsarin gaske a duniya masu iya haifar da barnar da ba za a iya zato ba.