A wani abu da za a iya kwatanta shi da mummunan lamari, mutane da dama sun yi asarar rayukansu a jihar Cross Rivers
An ce lamarin ya faru ne a unguwar Ekureku da ke karamar hukumar Abi ta jihar Cross River. Babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta Cross River, Dakta Iwara Iwara, ya tabbatar da haka.
Ya ce wata tawaga ta Calabar da ta kunshi kungiyar agaji ta Red Cross, da kuma ma'aikatar lafiya suna kan hanyarsu ta zuwa ga al'umma don tantance halin da ake ciki.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mutuwar cutar kwalara ce kuma mutane kusan 30 ne suka mutu.
Jaridar ta kara da cewa al’ummar Ekureku tana da kauyuka 10 da suka hada da Agbara , Ngarabe, Ekureku-be , Akpoha , Akare-for , Anong, Emenekpon , Etegevel, Egboronyi, Emegeh tana iyaka da wasu sassan jihar Ebonyi.
A halin da ake ciki, an ce al'ummar na fuskantar kalubale na ruwan sha.
An ruwaito wata majiya da ba a bayyana sunan ta ba na kusa da al’ummar ta na cewa an samu bullar cutar kwalara kwanaki biyu da suka gabata inda wasu mazauna kauyukan suka fara jin matsananciyar gudawa da rashin ruwa, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.