Reno Omokri, jigon jam’iyyar adawa ta PDP ya bayyana jerin wasu jihohi da yake da yakinin dan takarar PDP, Atiku Abubakar zai lashe kuri’unsu gaba daya a zaben 2023. Legit ya ruwaito.
Omokri, wanda tsohon hadimin tsohon shugaban kasan Najeriya Goodluck Jonathan ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter kamar yadda Legit.ng Hausa ta samo.
Jihohin da Atiku zai lashe zabe a 2023
A cewarsa, Atiku za iyi nasara a jihohin da bai cinye su akalla ko da kaso 25% ne zai kawo a zaben na 2023 mai zuwa.
Ga jerin jihohin da Atiku zai iya cin zabe ba makawa a cewar Reno Omokri.
1. Kano
2. Delta
3. Katsina
4. Akwa-Ibom
5. Kaduna
6. Kuros Riba
7. Jigawa
8. Bayelsa
9. Sokoto
10. Edo
11. Zamfara
12. Filato
13. Kebbi
14. Bauchi
15. Adamawa
16. Gombe
17. Taraba
18. Nasarawa
19. Neja
20. Benue