Fir'aunan zamanin Annabi Musa


Qur'ani da Bible sun yi bayanin mutuwar Fir'auna a cikin teku, amma Qur'ani ya kara haske akan cewa za'a adana gawar ta Fir'auna domin ya zama darasi ga al'umma da za su zo a bayan zamanin shi.

Shi wannan Fir'auna na lokacin Annabi Musa (a.s) sunan shi  FIR'AUNA RAMSES na 2.Kalmar Fir'auna dai yana nufin Sarki.

Ita dai wannan gawar an gano ta ne a 1881 a tsakanin wasu gawarwakin sarakunan kasar Masar da aka canja masu makwanci don fargaban kada a sace su,an sake gina wani kabarin na Fir'aunoni a  Deir al-Bahari a yammacin Luxor.Sabon kabarin Fir'auna Ramses dai yana a kabari mai lamba KV7.

A shekara ta 1974,sashen kula da kayakin tarihi na kasar Masar ta lura cewa gawar Fir'auna Ramses na 2 ta fara samun matsala,saboda haka aka yanke shawarar cewa a kai gawar kasar Faransa don ta sami kulawa daga kwararru.Ranar 26 ga watan Satumba 1976 wani jirgin yakin Sojan Faransa ya dira a filin saukan jiragen sama na Le Bouget a kasar Faransa dauke da gawar Fir'auna Ramses na 2,wanda ya sami tarbo na ni'ima da karramawa irin wanda ake yi wa shugabannin kasashe idan sun kai ziyara wata kasa.

Tarihi dai ya nuna cewa wannan Fir'aunan ya bar Duniya ne fiye da shekaru 3000.Amma gawar tana nan har yanzu a kasar ta Masar, watau Egypt.

Daga Isyaku Garba

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN