Wasu ‘yan bindiga sun kwace makaman jami’an NSCDC bayan sun kai masu farmaki
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kwace makamai daga jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) a Enugu.
Harin ya faru ne a daren Lahadi, 6 ga Nuwamba, yayin da jami'an 'yan sanda ke ba da tsaro ga rukunin gidaje na WTC a yankin Sabon Layi na Ogui na Garin Coal.
Yan bindigar sun raunata jami’an NSCDC tare da yin awon gaba da bindigogi.
An kai jami’an Civil Defence da suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa inda a yanzu haka suke samun kulawa.
Rubuta ra ayin ka