Wasu mahara sun kashe wani matashi mai suna Ashiru Nuhu Tofa a garin Minna na jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a kusa da ofishin ‘yan sanda na yankin a daren Asabar, 5 ga Nuwamba, 2022.
An tattaro cewa marigayin yana dawowa daga wurin budurwar tasa ne wasu mutane suka far masa.
An yi jana’izar sa ne a safiyar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, a gidan iyalansa da ke kan titin Katsina, a birnin Minna.
Rubuta ra ayin ka