Jama'a sun kama wani soji suka mika shi ga yan sanda bayan ya caka wa wani mutum wuka har Lahira a jihar kudu

Jama'a sun kama wani soji suka mika shi ga yan sanda bayan ya caka wa wani mutum wuka har Lahira a jihar kudu


Wani bala’i ya afku a karshen mako a Umuahia da ke jihar Abia, lokacin da wani soja da ke aiki da wani kamfanin gine-gine na kasar Sin a birnin ya daba wa wani mutum mai suna Offor Uchenna wuka har lahira.

Vanguard ta tattaro cewa an samu rashin jituwa tsakanin sojin da mutumin a tashar jirgin kasa dake Umuahia.

Wani mai shago a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sojan da aka bayyana sunansa da Saeed Sabo na runduna ta 82 ta sojojin Najeriya reshen Enugu, ya zare wuka ya daba wa wanda suke rigima a kirji.

Mutumin da lamarin ya rutsa da shi ya fadi cikin jini, inda aka kai shi cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Umuahia, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

“Babu wanda zai iya bayyana dalilin rashin jituwa tsakanin sojan da mamacin.  Tun daga nesa muke kallo suna ta ihu.  Suna ihu, sai sojan ya zare wata karamar wuka ya daba wa mutumin a kirji ya fadi.  An garzaya da shi asibiti inda ya rasu kafin su je FMC,” inji mai shagon.

Vanguard ta kuma tattaro cewa an kama sojan ne aka mika shi ga ‘yan sanda yayin da aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa an fara bincike kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN