Rikicin PDP: 'Na ci gaba, na daina damuwa da rikicin da ya dabaibaye jam'iyar,ba ni da wata damuwa'' - Atiku
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya daina damuwa da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Atiku ya yi magana kan rikicin PDP da aka dade ana fama da shi a wata hira da Muryar Amurka, VOA Hausa a cikin makon.
Dan takarar na PDP ya bayyana cewa ya ci gaba, inda ya kara da cewa a halin yanzu canjin shugabanci ba zai yiwu ba a jam’iyyar.
Ya ce, “Har yanzu ba mu sasanta lamarin ba. Amma mun ci gaba, ba ni da wata damuwa game da hakan kuma.
"Kuma a wannan mahadar, bai dace a yi maganar canjin shugabanci a jam'iyyar yayin da zabe ke gabatowa ba," Atiku ya kara da cewa.
Ku tuna cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da takwarorinsa na jihohin Benue, Enugu, Abia da Oyo; Samuel Ortom, Ifeanyi Ugwuanyi, Okezie Ikpeazu da kuma Seyi Makinde, sun yi kaca-kaca da Atiku a daidai lokacin da ake kira da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus.
Wike da sauran gwamnonin hudu da suka ji haushi sun dage cewa dole ne Ayu ya mika mulki ga dan Kudu.
Kokarin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi na sasantawa a tsakanin bangarorin ya ci tura yayin da jerin tarurrukan da Wike ke ci gaba da kai ruwa rana.