Kotun Kano ta jefa wasu mutane biyu zuwa Kurkuku bisa zargin bata sunan Ganduje

Kotun Kano ta jefa wasu mutane biyu zuwa Kurkuku bisa zargin bata sunan Ganduje


Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Kano ta tasa keyar wasu mutane biyu Mubarak Muhammad da Nazifi Muhammad Bala a zuwa gidan yari bisa zargin bata sunan gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Alkalin kotun, Aminu Gabari, ya tasa keyar mutanen biyu zuwa gidan yari bayan samunsu da aikata laifin.

Kamar yadda rahoton farko ya bayyana, mutanen biyu a cikin wani faifan bidiyo da suka wallafa a facebook, sun ce gwamna ba ya ganin fili sai ya sayar da shi, kuma yana barci da yawa.

Bayan da aka karanta wa wadanda ake tuhuma Rahoton Bayanin Farko, sun amsa laifin da FIR ta kunsa.

Mai gabatar da kara kuma babban lauyan gwamnati na ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Wada Wada, ya nemi a yi masa shari’a a kan wadanda ake kara.

Kotun ta same su da laifi kamar yadda ake tuhumar su sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga Nuwamba, 2022 don yanke hukunci.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE