Fusatattun matasa sun yi artabu yayin da babbar mota ta murkushe mata shida har lahira a Maiduguri
Wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga bayan da wata mota kirar tipper ta murkushe mata shida har lahira a hanyar Gubio, wajen birnin Maiduguri, jihar Borno. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:05 na safiyar ranar Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022, a Kaswan Fara, yankin Shagari Lowcost Estate lokacin da motar tipper da ke dauke da yashi mai kaifi ta kwace sakamakon gazawar birki.
Wani ganau mai suna Kola Fatai ya shaida wa Daily yrust cewa motar ta kutsa cikin motar daukar matan zuwa gona, inda ta kashe akalla 6 daga cikinsu.
Wani mazaunin garin, Iman Buba, ya ce wasu fusatattun matasa sun kona motocin tipper guda biyu, yayin da ‘yan sanda ke kokarin kwantar da hankula.
Masu zanga-zangar sun tare hanyar Gubio daga Maiduguri.
Wani shaidan gani da ido ya ce motar da ta haddasa hatsarin titin tana kokarin wuce wani tipa, amma ta rasa yadda za ta yi, kuma ta fada cikin motar daukar matan.
An baza jami'an tsaro a wurin domin shawo kan lamarin.
Rubuta ra ayin ka