Mutumin da ya kashe ’yar shekara 10 ya shiga hannu bayan shekara 56


Wani mutum mai shekara 73 da aka taba hukuntawa kan lalata da yara mata ya sake gurfana a gaban kotu kan tuhumarsa da bacewar wata yarinya ’yar shekara 10 a 1966 a birnin Massachusetts na kasar Amurka. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

A ranar Alhamis din makon jiya ne Mista Donald Mars ya gurfana a gaban kotun bisa zarginsa da kisan gilla ga wata yarinya mai suna Betty Lou Zukowski, wadda ta bar gidansu a yamamacin ranar 26 ga Mayun 1966, amma aka iske gawarta an yi mata duka bayan kwanaki a gabar kogin Westfield da ke garin West Springfield, kamar yadda mai gabatar da karar ya shaida wa Babbar Kotun Hampden da ke Springfield

An shigar da korafin rashin amincewa da zargin a madadin Mista Mars, kamar yadda kafar labarai ta Daily Voice HAMPDEN ta ruwaito Kuma lauyansa bai yi adawa da tsare shi ba tare da beli ba, sai dai yana iya neman a ba shi belin a wata rana.

“Duk da binciken ba zai dawo da Betty Lou ga iyalanta ba, ko ta dawo duniya ta rayu ta girma kamar kowane da ba, amma muna yi wa iyayenta da Betty Lou wannan gwagwarmaya ce don tabbatar da adalci,” in ji Babban Lauyan Gundumar Hampden, Mista Anthony Gulluni a wani taron manema labarai bayan zaman kotun.

Iyayen Betty Lou, Stanley da Mildred, sun rasu, amma hukumomi suna tuntubar sauran danginsu, in ji shi.

Marigayiyar ta bar gidan iyayenta ne bayan ta amsa kiran tarho daga wadda ta shaida wa iyayenta cewa kawarta ce, in ji Gulluni. Kuma iyayenta sun kai rahoton bacewarta cikin dare a ranar.

“Yara masu sun kifi sun gano gawar da aka yi wa duka aka dulmuya a cikin tabo mai tsawon kafa hudu da inci shida a Kogin Westfield da ke West Springfield,” in ji shi.

Ya ce, “Ofishin Babban Jami’in Gwaje-Gwajen Lafiya ya ce abin da ya jawo muturwata ya kunshi mugun dukan da aka yi mata a kai da fshewar kashin kwakwalwarta da kuma nutsar da ita a ruwa.”

Ya ce kuma saboda ta bar gidan cikin dadin rai, masu binciken suna da yakinin ta san wanda ya kai mata harin.

Ya ce, an binne ta a ranar 2 ga Yunin 1966, wadda ta zo daidai da ranar da ta cika shekara 11 a duniya.

Gulluni ya ce Mista Mars, wanda saurayi ne a lokacin rasuwar Betty Lou, an alkanta shi da kisan ne tun a 1997 amma ba a kama shi ba.

Ya ce an sake taso da maganar ce a ’yan watannin da suka gabata sai dai bai bayyana dalilan da suka sa aka alakanta kisan da Mars ba.

Bayanan kundin masu lalata da yara sun nuna an taba hukunta Mista Mars kan laifin fyade da cin zarafi da dukan wata yarinya ’yar kasa da shekara 14 a 1994.

Kuma an sanya shi a matakin na uku na masu lalata da yara, wanda hakan ne ake jin ya sa aka tado da wannan magana.

Adireshinsa na baya-bayan nan ya nuna yana zaune ne a Bedford. Ya halarci gabatar da shi a kotu ne ta bidiyo, sai dai bai ce uffan ba, inda ya rika girgiza kansa a lokuta da dama lokacin da mai gabatar da kara ya rika jero laifuffukan da ya aikata a baya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN