'Yan ta'addar ISWAP sun daina karbar Naira daga hannun manoma


Mayakan ISWAP sun daina karbar takardar kudin Naira daga hannun manoma da masunta da ke biyan su kudaden haraji, inda a yanzu suke karbar kudin CFA.  Shafin RFI ya wallafa.

Wannan dai, tasirin sakamakon da gwamnatin Najeriya ta dauka ne na sauya fasalin takardar kudin Naira da suka hada da Naira 200 da 500 da kuma 1000.

Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce, za a fara amfani da sabuwar takardar kudin Nairar a cikin watan Disamba mai zuwa kuma nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023, za a daina cin tsoffin takardun.

Rahotanni na cewa, wannan matakin da CBN ya dauka, ya jefa mayakan ISWAP cikin rudani a yankin Tafkin Chadi.

Yanzu haka mayakan na ISWAP na karbar CFA dubu 1 da 500 a kowane wata a matsayin haraji daga hannun wasu manoma da masunta.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE