Wani yaro dan shekara 8 da mahaifinsa ya yi garkuwa da shi ya shiga hannun jami’an tsaro a kasar Kenya inda ya sake haduwa da mahaifiyarsa da ke cikin damuwa.
Wanda ake zargin, Nemwel Ondari, ya sace yaron ne a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamba, bayan rashin jituwar cikin gida da matarsa, Everline Nandera.
An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da aka shigar a ofishin ‘yan sanda na Embakasi da misalin karfe 9:30 na safe, ta hannun mahaifiyar yaron.
A cewar wata sanarwa da hukumar binciken manyan laifuka-DCI ta fitar, inda ake zargin ya bukaci ya kuma yi barazanar kashe yaron da wuka idan matar ba ta yi sauri ba ta kai masa kudin fansa N180.000.
Wanda aka kama yana fuskantar bincike a hannun yan sanda.