Ikirarin kai wa ayarin Atiku hari karya ne – Rundunar ‘yan sandan Borno

Ikirarin kai wa ayarin Atiku hari karya ne – Rundunar ‘yan sandan Borno


Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta karyata labarin harin da aka kaiwa ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a jihar Arewa maso Gabas.

Jigon PDP kuma dan majalisar shugaban kasa a jam’iyyar Dino Melaye ne ya yi wannan ikirarin da safiyar yau.

Melaye ya ce an kai wa ayarin motocin Atiku hari ne a lokacin da ya ke tahowa daga wurin taron a jihar Borno a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, inda ya kara da cewa ‘yan banga daga jam’iyyun siyasa daban-daban sun lalata fiye da motoci 100 kuma an kwantar da mutane kusan 74 a asibiti.

Da yake mayar da martani kan hakan, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Sani Shatambay ya ce;

“Labarin harin da aka kai wa ayarin motocin Atiku Abubakar karya ne kawai, amma wani yunkuri ne na rudar da ‘yan Najeriya na karya da yaudara.

"Babu wani hari kan ayarin motocin Atiku."

Yan sanda sun kama Danladi Musa Abbas, dan shekara 32, saboda “kokarin da yayi na tarwatsa rakiyar dan takarar shugaban kasa a kan hanyar zuwa filin jirgin sama.”

Shatambay ya ce an kama wanda ake zargin ne da dutse kuma da “ganin ‘yan sanda ya shiga coci inda aka kama shi”.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, rundunar tana farautar sauran wadanda ke da hannu a harin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN