Type Here to Get Search Results !

Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da sakin Naira miliyan 50 ga hukumar Hisbah ta jihar


Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi ya amince da sakin Naira miliyan 50 ga hukumar Hisbah ta jihar.

Mallam Yahaya Sarki, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Birnin Kebbi, ranar Laraba.

Sarki ya ruwaito sakataren gwamnatin jihar (SSG), Babale Umar-Yauri yana cewa: “Sakin asusun ya kasance cika alkawarin da Bagudu ya yi a wajen bikin cika shekaru 20 da na kungiyar Hisbah ta Kebbi.

"Wannan karimcin na da nufin inganta ayyukan Hisbah don sanin irin gudumawar da hukumar ke bayarwa ga ayyukan jin dadin jama'a da kuma yaki da matsalolin al'umma." 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies