An kone matasa biyu da ransu bayan yunkurin fashi da makami a POS
Wasu fusatattun mutane sun kona wasu matasa biyu da ake zargi da yunkurin yi wa ma’aikatan Point of Sale (POS) fashi a jihar Enugu.
Lamarin ya faru ne a unguwar Independence Layout da ke kan titin Independence Avenue, wanda aka fi sani da Titin Bisala a ranar Laraba da yamma, 9 ga Nuwamba, 2022.
An tattaro cewa wadanda ake zargin ‘yan biyun sun yi yunkurin yin fashin ma’aikatan POS a yankin kuma mazauna yankin ne suka kama su.
Rahotanni sun ce ma’aikacin POS din ya daga karar yayin da ‘yan fashin da ake zargin sun zaro bindigogi suna neman kudi.
Kuwa da ya yi ta ja hankalin jama'a da suka bi mutanen da suka gudu suka kama su.
Kafin kona su, matasa sun yi masu tsirara, suka yi bidiyo, kafin su cinna musu wuta.
An kuma tattaro cewa mutanen da suka fusata ba su bari ‘yan sanda su kai su ofishinsu ba saboda sun ci karfinsu.
Wani faifan bidiyo da ke zagayawa a shafukan sada zumunta ya nuna daya daga cikin wadanda ake zargin da matasa ke yi masa tambayoyi.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda 'yan fashin ke konawa yayin da wasu tsirarun jama'a suka taru domin shaida lamarin.